Majalisar Dinkin Duniya tace ta fara rabon abinci da magunguna a yau Laraba, a kusa da yankunan da bala’in girgizan kasar Nepal ya auku, inda yanzu haka aka tabbatar da mutuwar mutane sama da dubu biyar.
Wannan tallafi na Majalisar Dinkin Duniya na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Nepal din ke cewa a yau laraba, za su kara kaimi wajen taimakon da ake baiwa wadanda ke bukatar abinci da ruwa da kuma matsuguni.
Yanzu haka, masu ayyukan ceto na ci gaba da kawar da fasassun bangorin da girgizar kasar mai karfin maki 7.8 ta haddasa.
A yammacin jiya Talata, wata tawagar kasar Faransa ta zakulo wani mutum daga burbushin gidansa da ya rushe a Kathmandu, babban birnin kasar, bayan da ya kwashe sama da sa’oi 80 a karkashin buragizan.
Wakilin Muryar Amurka da ke Nepal, Steve Herman yace masu bada agajin gaggawa na kasashen waje sun isa garin Sankhu dake gabashin Kathmandu a yau Laraba, sai dai wani wakilin kasar China yace da wuya a samu wani da rai.