NDLEA Ta Kama Muggan Kwayoyi a Filin Jirgin Abuja

Jami'ai Sun Kama Muggan Kwayoyi Saye Cikin Abinci a Filin Saukar Jiragen Sama Na Abuja

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya ta kama wani mai safarar miyagun kwayoyi mai suna Charles Obi, da nau'in hodar Iblis mai suna ‘methamphetamine’ da kimanin darajar kudin ta ya kai dala miliyan biyu.

Wanda a ka damken ya ce zai je Cambodia ne don aikin koyarwa amma wannan akasin ya rutsa da shi.

Kwamandan rundunar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na filin jirgin Hamisu Lawan ya ce wanda a ka damken ya lullube kwayoyin da kayan borkono da hakan zai hana karnuka masu bincike gano kwayar.

Hamisu Lawal, ya ce abin takaici shine yanzu haka an fara harhada irin wannan mummunar hodar Iblis a Najeriya.

Da zarar kammala bincike za a gurfanar da Charles Obi gaban kotu.

Kwanakin baya ma an kama wani mai safarar miyagun kwayoyi Kingsly Emenike Okolo, wanda ya shigo da hodar Iblis mai nauyin fiye da Kilogram 9 daga Sao Paulo zuwa Najeriya.

Hodar da darajar ta ta haura dala miliyan 4 an boye ta ne a cikin takalma masu araha.