Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abubuwan Koyi Ga Shugabannin Afirka Daga Shugaba Obama


Shugaba Barack Obama na Amurka yana ganawa da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a ofishinsa dake cikin fadar White House, Litinin 20 Yuli, 2015.
Shugaba Barack Obama na Amurka yana ganawa da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a ofishinsa dake cikin fadar White House, Litinin 20 Yuli, 2015.

Darussan da shugabannin Afirka ya kamata su koya gurin shugaban Amurka mai barin gado Barack Obama.

Ya yin da shugaban Amurka Barack Obama ke shirye-shiryen mika mulki ga magajin sa, Mr Donald Trump a ranar Juma’a mai zuwa, masana harkokin siyasa da difilomasiyya na ci gaba da fashin baki dangane da darrusan daya kamata shugabannin Afrika su koya daga salon mulkin Obama.

Lafazin canji da yunkurin jan matasa a jiki ta hanyar kafofin sadarwa na zamani da sada zumunci, zalakar zance da alkawarin rage dakarun Amurka dake fafatawa a ketare da kuma samar da tsarin kiwon lafiya da zai yi tasiri ga rayuwar talakawan Amurka, haka kuma da fatan inganta difilomasiyyar Amurka da kasashen duniya, baki daya na daga cikin abubuwan da shugaba Obama yayi amfani da su a yayin yakin neman zabe a shekara ta 2008.

Batun tada komadar tattalin arzikin Amurka na daga cikin al’amuran farko da shugaba Obama ya fara tunkara, inda ya amince da sanya makurdan kudade kamfanonin kere-kere na kasar a wani mataki na ceto su daga durkushewa.

Kokarin kyautata alakar Amurka da duniyar musulunci wani batu ne da gwamnatin Obama ta sanya a sahun gaba, inda har ma yayi alkawarin rufe sansanin Guantanamo Bay dake kasar Cuba, da rage adadin dakarun Amurka masu yaki a kasashen Iraqi da Afghanistan.

Shugaba Obama ya kai ziyara kasar Masar inda ya bayyana aniyar gwamnatinsa ta ‘daukar kasashen musulmi a matsayin abokan tafiya tare, a yayin da shugaba Obama ke shirin mika mulki ga wanda zai gashe a ranar Juma’a mai zuwa, masu kula da al’amuran siyasar duniya da difilomasiya na ci gaba da tsokaci kan salon mulkin Obama da kuma darussan da shugabannin Afirka ka iya koya.

Farfesa Kamilu Sani Fagge, na jami’ar Bayero dake Kano, yace babban darasin da za a iya kowa a gurin Obama itace, yadda ake ganin wani shugaba bakar fata ba zai iya yin komai ba sai ya tuntubi turawa an bashi shawarar yadda zaiyi, haka kuma ana ganin shugabanni bakaken fata basu iya komai ba sai mulkin kama karya, sai gashi mulkin Obama na nuna cewa duk wanda ya dage zai iya cimma nasara.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:56 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG