Babban Hafsan sojin kasa na Najeriya Laftanar-Janar Faruk Yahaya ya ce nasarar da dakarun kasar ke samu a yakin da suke yi da ‘yan ta’adda da sauran ‘yan bindiga na tattare ne da irin hadin gwiwar da suke yi da sauran hukumomin tsaro.
Janar yahaya ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyara Kwalejin horon sojoji, inda aka yaye rukunin manyan sojoji na 43.
Yayin da yake zagaya kwalejin wacce ke dauke da kayayyakin aiki na zamani da aka saka a kwalejin, babban hafsan sojin kasa na Najeriya ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa a duk atisayen da za a yi a kwalejin.
Karin bayani akan: Laftanar-Janar Faruk Yahaya, Faruk Yahaya, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, Nigeria, da Najeriya.
“Duk irin nasarar da dakarun kasa suka samu akan ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da sauran masu aikata manyan laifuka na da nasaba da hadin kai da sauran jami’an tsaron kasar.” Wata sanarwa dauke da sa hannun Darektan yada labarai Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ta ce.