Nan Da Mako Biyu Coronavirus Za Ta Sake Yawa Najeriya – Boss Mustapha

Masu Zanga-zanga a Najeriya

Kwamitin shugaban kasar Najeriya dake gudanar da bincike kan annobar cutar Coronavirus a kasar, ya yi hasashen cewa nan da mako biyu masu zuwa za a sake samun yaduwar cutar a fadin kasar, ganin yadda masu zanga-zanga ke bijirewa ka’idojin hukumomin lafiya na kare kai daga kamuwa daga cutar.

Sakataren gwamantin Najeriya Boss Mustapha, shine ya sanar da wannan gargadin a wani taron manema labarai kan cutar, inda ya ce za a sake samun karin a adadin masu kamuwa da cutar Covid-19 a kasar.

Daruruwan masu zanga-zangar kawo karshen rundunar yan sandan SARS wadanda ke yin gangami ba tare da mutunta kai’idojin hukumar lafiya na kare kai ba, ta hanyar kin amfani da kyellen rufe hanci da baki da rashin bada tazara a tsakanin al’umma.

Zanga-zanga

Tsohon shugaban hukumar dakile cututtuka masu yaduwa, “NCDC” Farfesa Abdulsalam Nasidi, ya yi gargadin cewa mundin ba a dakatar da zanga zanga a kasar ba, toh lalle a yi shirin rungumar duk abin da ka iya zuwa ya dawo.

Kusan makonni biyu kenan daruruwan mutane daga jihohi da dama a fadin kasar, ke zanga-zangar neman kawo karshen rundunar jami’an tsaro yan sandan SARS da aka yi korafin suna cin zarafin al’umma fiye da kima, wanda a wasu lokutan ya kan kai har da kisa.

Sai dai tun farkon fara zanga-zangar shugaban ‘yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu ya fito ya sanar da ruguza rundunar SARS, tare da maye gurbinta da wata sabuwar runduna da aka yiwa lakabi da suna SWAT.

Domin Karin bayani saurari rahotan Shamsiyya Hamza Ibrahim.

Your browser doesn’t support HTML5

Nan Da Mako Biyu Coronavirus Za Ta Sake Yawa Najeriya – Boss Mustapha - 3'06"