Dan takarar jam’iyyar Labor Party, Peter Obi, ya ce nan ba da jimawa ba, zai yi wa ‘yan Najeriya da sauran kasashen duniya jawabi.
Hukumar zabe ta INEC a Najeriya ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu.
Tinubu ya samu kuri’a 8,794,726, Obi, wanda ya zo na uku a zaben ya samu kuri’a 6,101,533.
Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya samu kuri’a 6,984,520.
“Dan takarar mataimakin shugaban kasa Dr. Yusuf Datti Baba-Ahmed na yi taron manema labarai na kasa da kasa a hedkwatar Labor Party da ke Abuja. Zan yi wa ‘yan Najeriya da sauran kasashen duniya jawabi nan ba da jimawa ba.” Obi ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba.
Manyan jam’iyyun siyasar kasar na bangaren ‘yan adawa ciki har da LP, sun nemi a yi watsi da sakamakon zaben, suna masu ikirarin an tafka magudi.
Hukumar INEC ta ce duk wanda yake da korafi da zaben ya je kotu, matsayar da Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya jaddada a sakonsa na taya Tinubu murna.