Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Gungun Mashahuran Mutane Ne Yake Juya Akalar Najeriya – Peter Obi


Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP a Najeriya, Mr. Peter Obi (Photo: AP)
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP a Najeriya, Mr. Peter Obi (Photo: AP)

Mr. Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabinsa a Cibiyar "Chatham House" da ke London a kasar Birtaniya ranar Litinin.

Dan takarar shugaban kasa karkashin tutar jam’iyyar Labor Party (LP) a zaben 2023 a Najeriya Mr. Peter Obi, ya yi ikirarin cewa wani gungun fitattun mutane ne yake juya akalar al’amuran kasar.

Mr. Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabinsa a Cibiyar "Chatham House" da ke London a kasar Birtaniya ranar Litinin.

"Chatham House," cibiya ce da ke bincike kan al’amuran da suka shafi manufofin kasashen duniya a fannin siyasa, tattalin arziki, ilimi da shugabanci da sauransu.

Yayin jawabin nasa mai taken; “Hange kan yadda za a sauya manufofi da ma’aikatun gudanarwa,” tsohon gwamnan jihar Anambrar ya kalubalanci ‘yan Najeriya, da su kalli taron na Chatham a matsayin wata dama da za su sauya tunaninsu.

“Najeriya kasa ce da ta makale a hannun wasu mashahuran mutane wadanda suke hawa mulki ta hanyar amfani da wasu dabaru, maimakon amincewar mutane, wanda hakan ya sa ba sa damuwa da biyawa jama’a bukatunsu.” Obi ya ce, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.

A cewar Obi, Najeriya na fuskantar “mummunar” matsalar tsaro wacce ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da asarar dukiyoyi.

“Tattalin arzikin Najeriya na cikin mawuyacin hali, ga tarin bashi yayin da ake satar mai da yawansa ba zai misaltu ba.

“Sau biyu Najeriya tana fadawa matsalar komadar tattalin arziki cikin shekaru shida, sannan matsalar karancin wutar lantarki, ta durkusar da kamfanoni da rayuwar jama’a ta yau da kullum.” In ji Obi.

Bisa jadawalin da ta fitar, a ranar 17 ga wtaan Janairu, Cibiyar ta "Chatham House" za ta karbi bakuncin shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, inda zai yi jawabi kan irin shirin da hukumarsa ta yi kan zaben.

Sannan a ranar 18 ga watan Janairu, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso zai gabatar da nasa jawabin.

A ranar 25 ga watan Fabrairu, Najeriya za ta gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya, sai kuma na gwamnoni da 'yan majalisun jihohi a ranar 11 ga watan Maris.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG