Shugaban kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yace mai yiwuwa ne Sudan ta Kudu ta zama member Majalisar Dinkin duniya mako mai zuwa. Sabuwar kasar, da za a kira Jamhuriyar Sudan ta Kudu, ta kamala shirin ayyana ‘yancin kai ranar Asabar. Jakaden kasar Jamus, Peter Wittig, shugaban kwamitin sulhu na wannan watan, ya bayyana ranar Talata cewa, yana kyautata zaton kwamitin Sulhu zai bada izini ga kasar Sudan ta zama memba ranar 13 ga watan nan na Yuli. Bisa ga cewarsa, yana yiwuwa babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’a a kai kashe gari. Idan aka amince, Sudan ta Kudu zata kasance member Majalisar Dinkin Duniya ta 193. Majalisar Dinkin Duniya tana tunanin girke rundunar wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu. Za a rantsar da shugaban kasar Sudan Salva Kiir ranar asabar bayan ya sa hannu a sabon kundin tsarin mulkin kasar. Arewaci da kudancin kasar sun yi yakin basasa na tsawon shekaru 21 wanda ya zo ga karshe a shekara ta dubu biyu da biyar bayan cimma yarjejeniya. Kudancin Sudan ya kada kuri’ar ballewa daga arewa a wata kuri’ar raba gardama da aka kada a watan janairu.
Nan ba da dadewa ba Jamhuriyar Sudan ta Kudu zata zama memba a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yace mai yiwuwa ne Sudan ta Kudu ta zama member Majalisar Dinkin duniya mako mai zuwa. Sabuwar kasar, da za a kira Jamhuriyar Sudan ta Kudu, ta kamala shirin ayyana ‘yancin kai ranar Asabar.