Wannan matakin na faruwa ne bayan da nakasassun suka gano cewa ana tafiyar hawainiya wajen fitarda wasu kudade miliyan 50 na CFA da gwamnati ta kebe dominsu a kasafin kudaden shekara.
Daruruwan mutanen dake fama da nakasa da suka hada da guragu, da makafi, da kurame ne suka hallara a farfajiyar ma’aikatar ministar al’umma yau Alhamis 2 ga watan Agusta, a matsayin matakin jan hakalin mahukunta akan maganar kudaden da dokokin kasa suke kebewa a kasafin kudaden kowacce shekara domin ayyukan inganta rayuwar nakasassu.
Dan Firoun Mounkaila, shine sakataren hadin guiwar kungiyoyin nakasassun Janhuriyar Nijer, ya ce kudaden da gwamnatin kasar ke warewa duk shekara don inganta rayuwar nakasassu, har yanzu basu gani a kasa ba.
A jajibirin wannan gangamin shugabannin kungiyoyin nakasassu sun gana da minister cigaban al’umma akan wannan batu sai dai ba su ji wata amsa mai gamsarwa ba mafari kenan da suka kira magoya bayansu akan su fito.
Daya daga cikin shugabannin dake kula da walwalar jama’a wanda ya fito da ofishinsa a madadin minister al’umma ya bukaci shugabannin nakasassu su hakura zuwa gaba, domin a cewarsa gwamnati na da niyyar share masu hawaye. To amma Malam Moussa Yakuba, daya daga cikin jagororin kungiyoyin nakasassu sun ba mahukuntan kasar kwanaki 20, idan ba biya masu bukatunsu ba, to za su yi gangamin da ya fi wanda suka yi.
Alkaluman da aka samu a sakamakon ayyukan kidayar jama’a da aka gudanar a shekarar 2012 sun yi nuni da cewa yawan nakasassu a Nijer ya haura daga 8, 0000 zuwa 715000 kwatankwacin kashi 1.4 daga cikin dari na yawan jama’ar wannan kasa, kuma galibinsu matasan da ba suyi karatu bane yayinda wadanda suka koyi sana’oin hannu ke fama da rashin jari lamarin dake kara tilastawa wasunsu rungumar sana’ar bara.
Ga karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5