Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Zimbabwe na Jiran Sakamakon Zaben Shugaban Kasa


Yanzu haka ‘yan kasar Zimbabwe na dakon sakamakon muhimmin zaben da aka yi a kasar, wanda wasu dayawa ke fatan ta yiwu, ya kawo sauyi ga tattalin arzikin kasar da ke fuskantar koma baya bayan mulkin tsohon shugaban kasa Robert Mugabe mai tsauri da yayi na tsawon shekaru 38.

A birnin Harare, wakilai masu sa ido akan zaben, sun bada rahoton cewa babu wata babbar matsala da aka samu jiya litinin a yayinda aka dakatar da kada kuri’a da maraice. Elmar Brok, shugaban wakilan kungiyar tarayyar Turai dake sa ido akan zaben, ya ce, a wasu sassan kasar komai ya tafi dadai wajen yin zaben amma a wasu wuraren abubuwa sun dagule.

Muryar Amurka ta kai ziyara a wasu rumfunan zabe a birnin Harare a yayinda ake shirin rufe su, kuma dukan su sun bayyana cewa mutane da yawa sun fito kada kuri’a, tsakanin kashi 85 zuwa 92 cikin 100. Jami’an zabe da wakilan jam’iyyu sun ce sun fuskanci kalubale sosai a jiya. Ko da yake, a jiya litinin, hukumar zaben kasar ta sanar da cewa ta kai karar wasu ‘yan takarar shugaban kasa su biyu wajen ‘yan sanda saboda sun cigaba da gudanar da yakin neman zabe har bayan lokacin da aka kayyade wato ranar Asabar. Duk da cewa hukumar bata bayyana ko su waye ba, ‘yan takarar manyan jam’iyyun kasar biyu sun yi yakin neman zabe a daren Lahadi.

Takarar tafi karfi tsakanin shugaban kasar mai ci Emmerson Mnangagwa wanda ya gaji shugaba Robert Mugabe a watan Nuwamba bayan da aka tilasawa Mugabe yin murabusa, da kuma shugaban hamayya Nelsom Chamisa, wanda ya bayyana damuwa a kan kuri’un yankunan karkara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG