NAKASA BA KASAWA BA: Hira Da Wani Mai Nakasa, Kocin Kungiyar Kwallon Kafa, Yuni 08, 2023

Souley Mummuni Barma

Wasannin motsa jiki na daga cikin jerin abubuwan da suka fara jan hankulan masu bukata ta musamman a ‘yan shekarun bayan nan a kasashen Afrika

NIAMEY, NIGER - A cikin shirin na wannan makon mun yi hira da Bachir Amma wani wanda ya tashi da sha’awar kwallon kafa tun ya na karami, kuma ya na daga cikin jerin nakasassun da ke horar da ‘yan wasa a jihar Agadez, wanda a yau shine Kocin kungiyar kwallon kafa ta NASARA.

Saurari cikakken shirin daga Souley Moumouni Barma: