Gwamnatin Najeriya ta ce saboda tabarbarewar tsaro a gabas ta tsakiya, musamman fadan da ake gwabzawa tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas zata kwashe ‘yan kasar da ke Lebanon.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Amb. Eche Abu-Obe, ya ce dama kasar ta kwashe ‘yan Najeriya da ke kudancin Lebanon zuwa babban birnin kasar Beirut.
“Tun a watan Agusta ofishin jakadancin Najeriya a Lebanon ke fitar da takardar gargadi da ba da shawara ga ‘yan kasar kan batun yadda zasu bar Lebanon ta hanyar jiragen fasinja da suke zuwa kasar.”
Sanarwar ta kara da cewa “ya zuwa yau dai babu wani dan Najeriya daya rasa ransa tun bayan barkewar fadan.”
Ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta tabbatar da cewa gwamnatin kasar na aiki da masu ruwa da tsaki don ganin an kare rayuwar ‘yan kasar a Lebanon har zuwa lokacin da za’a kwaso su zuwa gida Najeriya.