A ranar Asabar Hezbollah tace mayakan ta na yin fito na fito da dakarun Isra’ila a yankin kudancin kan iyakar Lebanon, inda dakarun Isra’ilan su ka ce sun kaiwa mayakan da Iran ke marawa baya hari a wani masallaci.
An dai ga karuwar rincabewar rikicin a yan kwanakin nan, ta irin hare haren da Isra’ila ke kaiwa kan muhimman wuraren Hezbollah a sassan Lebanon, yayin da dakarun dake yaki ta kasa suka gudanar da samame a kusa da kan iyaka, lamarin da ya kusa sauya al’amurra akan iyakar zuwa yaki gadangadan.
A labarin farko farko da aka bayar na harin da Izra’ila ta kai ta sama, kan yankin Arewacin Tripoli a kazancewar da yakin yayi a baya bayan nan, kungiyar mayakan Hamas a Palasdinu, tace, mummunan harin rashin imani da aka kai kan sansanin yan gudun hijira na Beddawi ya kashe wani kwamanda mai suna Saeed Attallah Ali da maidakin shi da yayan shi mata su biyu a ranar Asabar.
Kazancewar da yakin yayi a makon nan, ya hada da hari na biyu na makami mai linzami da Iran ta kai kan Isra’ila, kara kaimin hare haren rokokin da hari ta sama da Hezbollah ke kaiwa, da kawayen Iran suka dauki nauyin su har daga Yemen, da ya zo kwanaki kafin cikar shekara guda da harin da Hamas ta kaiwa Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.
A wani yanki na Beirut, Ibrahim Nazzal, wanda daya ne daga cikin daruruwan dubban mutanen da rikicin ya dai dai ta, ya bayyana cewa, yana son a dakatar da yakin domin su koma kasar su. Yace, ‘duk mun rasa gidajen mu. Ban san inda zamu nufa ba daga nan’’
Kusan shekara guda da fara yaki a zirin Gaza, da harin da Hamas ta kai ya tsokano, a yanzu Izra’ila ta karkata akalar ta zuwa arewaci, inda take hankoron ganin dubban Yahudawan da rokokin da Hezbollah ta rika harbawa,ya dai dai ta sun koma gida.
Sojojin Isra’ila sun kaddamar da wani gagarumin jerin hare hare kan muhimman wuraren Hezbollah a yankin Lebanon, da ya hallaka mutane sama da dubu daya da 110 tun a ranar 23 ga watan Satumba.
A gefe guda kuma, Hezbollah tace da sanyin safiyar Asabar mayakan ta sunyi gumurzu da dakarun Isra’ila a wani yanki na kan iyaka, bayan labarin ta na farko, na tilastawa sojoji komawa da baya.
Dakarun Isra’ila sunce sun kashe mayakan Hezbollah su 250 a yankin dake kan iyaka cikin wannan makon, suka kuma kai hari a ranar Asabar kan wata cibiyar mayakan a cikin wani masallaci a garin Bint Jbeil.
Dandalin Mu Tattauna