Wani harin Isra’ila ta sama a kasar Lebanon, ya hallaka wani ba-Amurke daga garin Dearborn na jihar Michigan, a cewar ‘yar mutumin da abokinsa da kuma ‘yar majalisa mai wakiltar yankin da ya fito.
A jiya Laraba, ofishin ‘yar majalisar wakilan Amurka ta jam’iyyar Democrat Rashida Thiab ya bayyana cewar yana tattaunawa da iyalan Kamal Ahmad Jawada, inda ya kara da cewa dan mazabar ‘yar majalisar Amurka ‘dan asalin Falasdinu ne kuma shi ba-Amurke ne.
Sanarwar da ‘yar mutumin, Nadine Jawad ta fitar ta bayyana cewa harin Isra’ila ta sama a kasar Lebanon ne ya kashe mahaifinta a Talatar da ta gabata “yayin da yake kokarin ceton wasu mutane.”
Ta kara da cewa a kwanakinsa na karshe a duniya, mahaifinta ya zabi ya zauna kusa da wani asibiti yana taimakon tsofaffi da nakasassu.
“Muna matukar alhinin mutuwar Kamal Ahmad Jawada kuma zuciyoyinmu na tare da iyali da abokansa. Mutuwarsa abin tashin hankali ce, kamar ta dimbin farar hular da suka mutu a Lebanon,” a cewar kakakin fadar White House a wani sako na daban da aka fitar ranar Laraba.
Hare-haren rundunar sojin Isra’ila na baya-bayan nan ya hallaka daruruwan mutane, tare da jikkata dubbai da kuma raba fiye da miliyan da gidajensu.
Isra’ila tace tana harin mayakan kungiyar Hezbollah ne masu samun goyon bayan kasar Iran.
Dandalin Mu Tattauna