A yayin da ake ci gaba da tafka muhawara kan batun zargin da shugaban mulkin sojin Najeriya ya yi a game da cewa gwamnatin Najeriya na hada kai da Faransa don yiwa Nijar din zagon kasa, ministar harkokin wajen Najeriya, Amb. Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa, gwamnatin kasar zata hada gwiwa da kasar Sin wajen fara kera makaman yaki da matsalolin tsaro cikin gida a maimakon a ci gaba da shigowa da su sakamakon wasu matsalolin da ake fama da su wajen sayo daga waje.
Amb. Tuggar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin takwaransa na kasar Sin, Wang Yi, a Abuja yau Alhamis ya na mai cewa, zuwan Wang Yi, ya nuna mahimmancin da kasar Sin ke baiwa Najeriya game da harkokinsu da Afrika.
Yarjejeniyoyin da Najeriya ta cimma tare da Kasar Sin a fannin kasuwanci, tsaro, horaswa, ci gaban al’umma, tattalin arziki, kera makamai, al’adu, ababen more rayuwa kamar layin dogo, baya ga wasu muhimman bangarori.
A cewar Amb. Tuggar, zuwan Wang Yi, ya kara tabbatar da cewa shimfida layin dogo daga Kano zuwa birnin Maradi na jihar Nijar, Kano da Jigawa, kuma ana ci gaba da aiki a kan yadda kasar Sin zata kara zuba kudadde domin ganin an gama aikin cikin hanzari, kuma a halin yanzu an kai kaso 40 cikin 100 na aikin, yana mai cewa duk da cece-kucen da ake tsakanin kasashen Nijar da Najeriya, ba’a fasa aikin ba kuma ita Nijar tana kan yin tashoshin karban kwantena-kwantena ma.
Ministan ya kuma jaddada aniyar gwamnatin Najeriya na aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma da kasar Sin yayin ziyarar aiki da shugaba Bola Tinubu ya kai a watan Satumba na shekarar 2024.
Ziyarar ministan harkon wajen kasar Sin a Najeriya wato, Wang Yi, na nufin karfafa huldar dake tsakanin kasashen Najeriya da kasar Sin tare da kara kaimi ga hadin gwiwa a muhimman fannoni da suka hada da tsaro, kasuwanci da cinikayya ciniki da zuba jari, kiwon lafiya, fasaha da raya ababen more rayuwa in ji, Amb. Tuggar.
Da yake gabatar da jawabin bude taron ganawa tsakanin shi da takwarar sa na kasar Sin, Amb. Yusuf Tuggar, ya yi alkawarin cewa zasu kara karfafa alaka tsakanin kasashen biyu, ya na mai yin misali da ziyarar da shugaba Tinubu ya kai kasar Sin a watan Satumbar 2024 inda aka rattaba hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna guda hudu tare da jaddada kudurin ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar da ya ce suna matakai daban-daban na aiwatarwa.
A yayin da ake ganawar, ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, wanda wannan shi ne ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka a wannan shekarar, ya ce ya zo ne domin ci gaba da tattaunawa a kan muhimman batutuwa da aka cimma a yayin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da nahiyar Afirka wato FOCAC, wanda aka gudanar a shekarar da ta gabata, inda ya bayyana aniyar kasar Sin na inganta dangantakarta da Najeriya.
Ministan na kasar Sin ya isa Najeriya ne a ranar Laraba da misalin karfe 7:15 na yamma agogon kasar, inda ya samu kyakkyawar tarba daga babban sakataren ma'aikatar harkokin wajen kasar, Ambasada Dunoma Umar Ahmed, da wasu manyan jami'an gwamnati ciki har da jakadan kasar Sin dake Najeriya. Ambassador Yu Dunhai.
A yayin ziyarar nan dai ana sa ran, Wang Yi zai kara ganawa da manyan jami'an gwamnati, inda za su tattauna batutuwan da suka shafi duniya baki daya, tsaron yankin, da kuma ci gaban tattalin arziki.
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da manyan jami'an diflomasiyya a Abuja a ranar 8 ga Janairu, 2025 kuma ziyararsa ta jaddada aniyar kasar Sin na inganta hadin gwiwarta da Najeriya, da kara karfin dangantaka tsakanin kasashen biyu domin tabbatar da ci gaba, samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin kasashen Afrika ta yamma.
Saurari cikakken rahoto daga Halima AbdulRauf:
Your browser doesn’t support HTML5