Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambassada Yusuf Maitama Tuggar, yace gwamnatin kasarsa na bukatar a tsawaita yarjejeniyar AGOA, wacce ta baiwa gwamnatocin kasashen kudu da hamadar saharar Afrika damar yin hada-hada a kasuwannin Amurka ba tare da biyan haraji ba.
A wata hira da yayi da wakilin Muryar Amurka Victor Mathias, Tuggar wanda ke jagorantar shirin aiwatar da sabuwar manufar kasashen ketare da Shugaba Tinubu ya kirkiro, yace yarjejeniyar AGAO zai taimaka wa tattalin arzikin kasashen Afirka wanda Amurka ta yi musu rangwame wurin biyan haraji domin ya basu daman shigo da kayayyaki da aka sarrafa a Afirka kasuwannin Amurka.
“Muna son mu ga majalisarsu a nan ta kara tsawon yarjejeniyar domin wa’adinsa ya cika. Sai kuma Majalisar su ta duba kafin ta yanke shawarar ko ta kara ko ta dakatar da shi. Mun zo mu kara jadada musu muhimmancin wannan musamman a yanzu da tattalin arzikin kasashen Afirka da dama ke fama.
Ya kara da cewa daman Najeriya shugaba ce a Afirka kuma duk inda aka samu daman yin abunda zai taimaka wa Afirka, muna yi.
Dandalin Mu Tattauna