Shugaban yana musanya kalamu ne da shugaban hukumar kasuwanci ta duniya ko WTO Jakada Roberto Azevedo wanda ya ka ma shugaba Buhari ziyara a fadarsa ta Aso Rock dake Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Shugaba Buhari ya bashi tabbacin kasancewar Najeriya cikin harkokin kasuwancin duniya duka da faduwar farashin man fetur a duniya.
Shugaba Buhari yace "ina farin ciki cewa kasan irin halin da muka samu kanmu, kamar yanayin tattalin arzikinmu da kayan da muke anfani dasu da dai sauransu. Duk da matsalolin mun kuduri aniyar cigaba da rungumar harkokin kasuwanci na kasa da kasa kamar yadda WTO ta tsara" inji shugaba Buhari.
Shugaban WTO din ya bayyana farin cikinsa da Najeriya yadda take cigaba da yin muamala da kafofin kasuwancin kasashen waje har ya kara da cewa nan ba dadewa ba hukumar zata fara tattaunawa da Najeriya akan wasu abubuwa da suka shafeta kaman inganta kananan masana'antu da matsakaita ko SME wadanda aka tabbatar su ne suka fi daukan ma'aikata a kasashe masu tasowa.
Najeriya nada muhimmiyar rawa da zata takamusamman a wannan lokaci mawuyacin hali. Yace farashin man fetur na faduwa lamarin da ya sa kasuwa dake tasowa da sun fara durkushewa.