An kashe Murtala a ranar 13 ga watan Febrairun shekarar 1976 a lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa barikin soji na Dodan Barack da ke Legas.
Wasu sojoji ne a karkashin jagorancin Lt Col. Buka Suka Dimka suka kashe tsohon shugaban Najeriyar.
An kashe shi ne tare da mai kula da lafiyarsa Akintunde Akinsehinwa, a lokacin yana mai shekaru 37.
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ne ya maye gurbinsa wanda ya aiwatar da shirin sa na mika mulki ga farar hula.
A ranar 30 ga watan Yuli Gen. Murtala ya fara shugabantar Najeriya bayan da aka hambarar da gwamnatin Gen. Yakubu Gowon a lokacin da ya ke halartar taron kungiyar kasashen Afrika.
Shi dai Murtala mutum ne wanda ‘yan Najeriya ba za su yi saurin mantawa da shi saboda irin jarumtaka da ksihin kasa da ya nuna a lokacin mulkinsa.
A zamaninsa rahotanni sun nuna cewa wadanda su ke adawa da shi ma sukan yaba mai duk da cewa ba sa jituwa.
Saurarin wannan hirar Dr. Sa'idu Ahmad Dukawa da Sahabu Imam Aliyu wanda ya yi magana kan dalilan da ya sa ‘yan Najeriya ba za su yi saurin mantawa da Gen. Murtala Muhammad ba: