Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Mika Manyan Sojojin Najeriya Ga EFCC


Wasu sojojin Najeriya
Wasu sojojin Najeriya

Rundanonin sojin sama da na kasa sun mika wasu manyan sojoji zuwa ga hanun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, a ci gaba da binciken da ake yi kan badakalar kudaden sayen makamai.

Tun bayan hawan wannan sabuwar gwamnati aka fara binciken kudade sama da dala biliyan 2.1 da ake zargin an karkata akalarsu.

Kudaden an ware su ne domin sayen makaman da za a yaki kungiyar Boko Haram, lamarin da ya cutura.

A baya aka kama tsohon mai baiwa shugaba shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki wanda ake zargi kudaden sun fita daga ofishinsa.

Wannan badakala ta ja hankula mutanen Najeriya da dama ganin irin yawan kudaden da kuma irin halin tsananin rayuwa da mutane arewa maso gabashin Najeriya suka shiga, tun bayan da kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hare-hare a yankin.

Saurari wannan rahoto na Hassan Maina Kaina domin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG