Najeriya Za Ta Bi Kadun ‘Yan Kasar Da Rikicin Afirka Ta Kudu Ya Shafa

Wasu 'yan Afirka ta Kudu sun afkawa wani 'dan Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta bi kadun `yan kasar da aka jikkata tare da kona musu dukiya a kasar Afirka ta kudu, biyo bayan rikicin kyamar baki.

Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu cikakken bayani akan abin da ya faru a rahotan da jami’an jakadancinta suka aika mata. Rahotan ya nuna cewa babu wani ‘dan Najeriya da ya rasa ransa a rikicin kyamar baki da akayi a baya bayan nan a Afirka ta Kudu.

Sai dai kuma akwai mutane masu yawa da aka Konawa gidajensu da guraren sana’arsu wanda gwamnatin Najeriya ta ce zata bi kadunsu.

Ministan ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Khadija Bukar Abba Ibrahim, tace Najeriya zata matsawa gwamnatin Afirka ta Kudu, domin ta dauki mataki kan mutanen da ke nuna kyamar baki wanda yake kaiwa ga kisa da kuma barnata dukiyoyi.

Shima jakadan Afirka ta Kudu a Najeriya, Mista Lulu Louis Mnguni, yace kasarsa ta damu matuka akan abin da ya faru kuma tana daukar matakai don magance matsalar.

Masana harkokin difilomasiya irin su ambasada Sulaiman Dahiru, na ganin ya kamata gwamnatin Afirka ta Kudu ta biya ‘yan Najeriya diyya, tare da hukunta wadanda suka haddasa rikicin muddin ana son magance matsalar kyamar baki a kasar.

Wannan dai bashi ne karon farko ba da ake kaiwa ‘yan Najeriya hari a kasar Afirka ta Kudu, inda a baya dai anyi zargin cewa an kashe mutane 20 a irin wannan tashin hanklin.

Domin karin bayani saurari rahotan Sale Shehu Ashaka.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Za Ta Bi Kadun ‘Yan Kasar Da Rikicin Afirka Ta Kudu Ya Shafa - 2'19"