Rahotan kungiyar Amnesty International mai rajin kare hakkin bil Adama ta fitar ya nuna cewa sojojin Najeriya na yin kisan gilla ga ‘yan kasar a shiyyar Arewa maso Gabas da kuma masu fafutukar ballewa daga Najeriya a yankin Kudu maso Gabas.
Daraktan watsa labarai a hedikwatar sojojin Najeriya, Birgediya janal Rabe Abubakar, yayi watsi da zargin da kungiyar ta Amnesty International ta yi cewar sojoji da sauran jami’an tsaro na take hakkin bil Adama. Inda yace wannan zargi ne wanda bashi da tushe ko makama, domin sojojin Najeriya na iya bakin kokarinsu wajen ganin an samar da zaman lafiya mai dorewa.
Kan batun zargin cewa sojoji na kashe masu fafutukar kafa ‘kasar Biafra a Kudu maso Gabashin Najeriya. Janar Abubakar yace ba gaskiya bane, “Ya za a yi soja wanda aka koya masa zuwa ya kwantar da hankali sannan kuma ya aika hakan.” Ya ci gaba da cewa aikin soja ne ya kare hakkin ‘yan kasarsa, kuma duk wanda ya fito domin tayar da hankali a ‘kasa dole ne a taka masa birki.
Sanannen lauya mai fafutukar kare hakkin bil Adama a Najeriya, Barista Yakubu Sale Bawa, ya zargi Amnesty International da son haddasa rudani a cikin Najeriya. inda yace kungiyar ba ta fadawa duniya gaskiya da abubuwan da suke faruwa a zahiri. Ya kuma ce suna amfani da fadin karya ne domin samun kudi.
Shima masananin tsaro Dakta Bawa Abdullahi Wase, yayi Allah wa dai da wannan rahoto na kungiyar Amnesty International, yace Najeriya tana da kundin tsarin mulkin ta, kuma maganar cewa suna fafutukar ‘yancin dan Adama wannan shirye ne kawai suke. Daga karshe yayi kira da kada a rika kula da abin da suke fada.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum