Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Gudanar Da Zaben 'Yan Majalisa a Rivers


Election official count gubernatorial ballot papers at the end of voting in one of the polling station in Lagos, Nigeria, April 11, 2015.
Election official count gubernatorial ballot papers at the end of voting in one of the polling station in Lagos, Nigeria, April 11, 2015.

Hukumar zaben ta INEC a najeriya za ta tura jami’ai 753 don kammala zaben dan Majalisar tarayya da na Jiha a mazabar  Ecthe dake jihar Rivers.

Za’a gudanar da zaben ne a ranar Asabar mai zuwa, wato 25 ga watan Fabrairu, kuma zai kasance mai matukar muhimmanci, lamarin da ya sa dauki tsauraran matakan tsaro domin mazabar ce ta karshe da ta gagari a gudanar da zabe a jihar ta Rivers dake kudu maso kudancin Najeriya.

Jihar river ta yi kaurin suna wajen tashin hankalin a duk lokacin da za a gudanar da zabe

Ko a zaben watannin baya da aka yi, an kashe wani jami'in 'yan sanda mai suna DSP Alkali Muhammeda wanda aka masa kai da tare kuma da kashe jami’in da ke rufa masa baya.

Wannan zaben ya jawo rundunar 'yan sanda ta Najeriya ta damke da kuma korar shida daga cikin jami’anta dake tawagar Gwamna Ezenwo Wike da aka samu da harba bindiga kuma hakan ya jawo hargitsa a wata cibiyar zabe.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ta INEC Nick Dazang ya bayyana cewar zamanin nadi ya shude kuma abin takaici ne ace a wannan karni har yanzu mutane na yin haka domin cimma burinsu.

Domin karin bayani sai a saurari rahoton Nasiru Adamu El-hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG