A cewar daraktan ma’aikatar ‘yan Kwana-kwana ta jihar Gombe, Solomon Lakwande, gobarar ta samo asali ne daga wutar lantarki, sun gano hakan ne biyo bayan binciken da su kayi. Ya kuma tabbatar da cewa mutane bakwai ne suka rasa rayukansu.
Domin rigakafin afkuwar irin wannan mummunar gobara ma’aikatar ‘yan Kwana-kwana na wayar da kan mutane ta hanyar amfani da Masallatai da Majami’u da kuma gidajen radiyo, kan cewa mutane su rika kula da duk kayayyakin wutar lantarki, kuma idan za a kwanta a rika kashe duk wasu abubuwan da suka kamata – a cewar Solomon Lakwande.
Aliyu Haruna, shine magidancin da wannan gobara ta yiwa barna, yace gobarar ta tashi ne a gidan amaryarsa yayin da yake can gidan uwargidansa, kasancewar yana da gidaje biyu.
Domin karin bayani ga rahotan Abdulwahab Mohammad.
Facebook Forum