NAJERIYA: Za a Samar Da Kayayyakin Kariya Ga Ma'ikatan Kiwon Lafiya

Hukumomi a Najeriya sun yi alkawarin samar da kayayyakin kariya ga ma’aikatan kiwon lafiya biyo bayan kara yawan kamuwa da COVID-19 tsakanin ma’aikatan. 

A hirar shi da manema labarai a Abuja, Chikwe Ihekweazu, babban darektan cibiyar yaki da cututtukia masu yaduwa ta Najeriya, ya fada a jiya Litinin cewa, ma’aikatan kiwon lafiya 75 ne gwaji ya tabbatar da sun kamu da cutar. Ya kuma bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki.

Ihekweazu ya yi kira ga ma’aikatan lafiyar da su yi taka tsantsan kana su dauki duk wanda ya je gaban sun tamkar wanda ya ke dauke da coronavirus, har sai sun tabbatar ba ita bace. Ya yi kashedi cewa har yanzu akwai barazanar kamuwa da cutar.

Ihekweazu ya kuma ce cibiyar ta NCDC nan ba da dadewa ba zata samar da na’urar gwajin a asibitoci da dama a matsayin karin matakan kariya.

kwararru-a-hukumar-who-na-binciken-asalin-korona-a-kasar-china

codvid19-najeriya-za-ta-kashe-n400b-kan-rigakafi

mutane-fiye-da-miliyan-75-suka-kamu-da-covid-19-a-fadin-duniya

Kamfanin dillancin labarai na Anadolu yace sama da ma’aikatan kiwon lafiya 800 ne suka kamu da coronavirus a Najeriya ya zuwa watan Yuni, a cewar ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire.

Kungiyar likitoci ta Najeriya ta tabbatar da mutuwar a kalla likitoci 20 da suka kamu da cutar Korona a cikin mako guda watan da ya gabata.

Cibiyar tattara bayanan Korona na Jami'ar John Hopkins

Cibiyar tattara bayanan Korona na Jami'ar John Hopkins

Kawo yanzu, sama da mutane 131,000 suka kamu da COVID-19, yayinda 1,607 kuma suka mutu, bisa ga kiddigar cibiyar sa ido kan yaduwar cutar Korona ta Jami'ar Johns Hopkins da ke Amurka.