Najeriya Ta Yi Cefanen Jiragen Yaki Daga Italiya

Wani jirgin yakin Najeriya (Wannan hoto an yi misali ne da shi)

Najeriya na fama da matsaloli na tsaro ciki har da barayin daji da suka addabi yankunan arewa maso yammacin kasar.

Rundunar Sojin saman Najeriya ta yi cefanen jiragen yaki na sama daga kasar Italiya.

Shugaban Hafsan Sojojin Sama, Air Marshal Hasan Abubakar, ya jagoranci wata tawagar kwararrun sojojin sama domin samun jiragen yakin da helikwopta daga kamfanin Messrs Leonardo S.p.A a kasar ta Italiya.

Wata sanarwa da sojojin saman suka fitar dauke da sa hannun Daraktan Hulda da Jama’a da Bayani na Sojojin Sama, Air Commodore Olusola Akinboyewa, a ranar Lahadi a Abuja ce ta bayyana hakan.

Najeriya na fama da matsaloli na tsaro ciki har da barayin daji da suka addabi yankunan arewa maso yammacin kasar.

Mafi akasarin farmakin da ake kai wa ‘yan fashin dajin don kassara ayyukansu a jihohin Sokoto, Zamfara da Katsina daga sama ne.

Jiragen sun hada da jiragen yaki 24 na M-346 Fighter Ground Attack (FGA) da karin helikwopta 10 na AW-109 Trekker.