Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mummunan Hari Kan Masu Maulidi A Kaduna Ya Haddasa Rudani


 Jirgin yaki
Jirgin yaki

Bayan wani mummunan hari da ake zargin wani jirgin sojojin Najeriya ne ya kai akan wasu fararen hula a jihar Kaduna, lamarin ya haddasa rudani da zaman zullumi.

A jiya ne akai zargin wani jirgin soji ya kai tagwayen hare-hare a kan wasu fararen hula dake gudanar da bikin maulidi a wani kauyen dake yankin karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna.

Harin anyi zargin ya haddasa rasa rayukan gomman mutane, wasu kuma da dama suka sami raunuka nau'o'i daban daban, a halin yanzu kuma ana kula dasu a Asibitin Barau Dikko dake birnin kaduna.

A na cikin wannan zaman zullumi ne kuma hedkwatar sojojin saman Najeriya, ta nesanta kanta daga kai wannan hari.

Kakakin sojojin saman Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet, ya bayyana cewa jiragen yakinsu cikin sa'o'i ashirin da hudun da suka gabata ba wani farmaki da suka kai a ko'ina cikin jihar kaduna.

Commodore Gabkwet, ya yi bayanin cewa cikin jami'an tsaron dake fafatawa da yan bindigar jihar kaduna, ba sojojin sama ne kadai suke amfani da jirgin kai farmaki maras matuki ba.

Yakarkare da cewa sojojin sama suna tsananta bincike, bin diddigi da kuma tattara sahihai kuma ingatattun bayanan sirri kafin kai farmaki.

Kokarin da wakilin Muryar Amurka a Abuja ya yi don jin ta bakin rundunar sojin kasa da ke jagorantar farmakin yaki da yan bindiga a a shiyyar kaduna bai nasara ba, kokarin da ya yi na neman karin bayani daga kakakin sojojin janar onyeama Nwachukwu bai yiwu ba, kuma layin wayarsa ba ya shiga.

Rahotannin dake fitowa daga jihar kaduna na nuna tuni gwamnatin jihar ta mika sakon ta'aziyya da jaje ga wadanda Iftila'in ya rutsa da su, sannan ta tabbatar da za a gudanar da bincike.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG