Najeriya Ta Yi Asarar Dala Biliyan 40 Sakamakon Rashin Tsaro A Shekarar 2020

  • Murtala Sanyinna
Najeriya ta yi asarar zunzurutun kudi har dalar Amurka biliyan 40.6 a shekarar 2020 sakamakon kalubalen tsaro, a yayin da ayukan kungiyar Boko Haram, ISWAP da ‘yan bindigar daji suka addabi kasar.

Rahoton Cibiyar Bincike Da Nazari Kan Tattalin Arziki da Zaman Lafiya ta duniya da ke birnin Sydney da ta fitar a watan nan na Yunin shekara ta 2021, ya bayyana cewa tashe-tashen hankula sun haifar da mummunan illa ga tattalin arzikin duniya, tare da asarar kudi dalar Amurka kusan tiriliyan 15 da aka kashe wajen sayen kayayyakin yaki da matsalar tsaro a duk fadin duniya.

Rahoton ya ce tasirin na tashe-tashen hankula kan tattalin arziki a fadin duniya na shekara ta 2020 ya karu da kashi 0.2 cikin dari, idan aka kwatanta da adadin kudin da aka yi asara a shekarar da ta gabace ta 2019, da suka kama dala biliyan 32.5, da gwamnatoci suka kashe wajen sayen makamai da sauran kayan aikin jami’an tsaron cikin gida.

Rahoton ya saka Najeriya daga cikin jerin kasashen da suka fi karancin zaman lafiya a duniya, inda take kasa ta 146 daga cikin kasashe masu zaman lafiyar 163.

Rahoton ya kuma bayyana cewa tasirin tashe-tashen hankula a Najeriyar, ya haifar mata da asarar kudi dalar Amurka biliyan 40.6, wanda a cewar rahoton, adadin ya karu idan aka kwatanta shi da na shekarar 2019.

Sansanin 'yan kungiyar Boko Haram da dakarin hadin gwiwa suka kai farmaki (Hoto: Shafin Twitter Na Dakarun Najeriya)

Sansanin 'yan kungiyar Boko Haram da dakarin hadin gwiwa suka kai farmaki (Hoto: Shafin Twitter Na Dakarun Najeriya)

Ya bayyana cewa asarar da kasar ta yi ta bangaren tattalin arziki, ya kumshi makudan kudaden da ta ke kashewa ga rundunar soji da sauran al’amuran da tashe-tashen hankula suka haifar, kamar mutuwa, kone-kone da kuma dauki ga ‘yan gudun hijira.

Karin bayani akan: Abubakar Shekau, Amurka, Abu Musa Al-Barnawi, jihar Borno, ISIS, ISWAP, UNHCR, Boko Haram, Bakura Modu, Nigeria, da Najeriya.

A bangaren tsaro da zaman lafiyar al’umma, rahoton ya saka Najeriya a zaman daya daga cikin wurare mafi karancin zaman lafiya a doron kasa, inda ta ke cikin kasashe 26 da suka fi tashe-tashen hankula, a yayin da kuma ta ke daya daga cikin kasashe 46 a haujin girke dakarun soji cikin al’umma.

Najeriya dai ta yi fama da ayukan ‘yan kungiyar Boko Haram a Arewa maso gabas, a yayin da kuma ‘yan bindigar daji suka addabi jama’a da hare-hare, kisan gilla da satar jama’a domin karbar kudin fansa a Arewa maso yamma a shekarar da ta gabata.

Fulani masu garkuwa da mutane

To sai dai masu fashin baki na gani ba abin da ya sauya a wannan shekara ta 2021, sai ma kara uzzura da suke ganin kalubalen tsaron yayi, tare da samuwar ayukan wasu ‘yan ta da kayar baya a kudancin kasar, bisa da’awar fafutukar neman ballewa daga Najeriyar.

Wata Kungiya Mai Alaka Da IS Ta ce Shugaban Boko Haram Shekau Ya Mutu

Your browser doesn’t support HTML5

Wata Kungiya Mai Alaka Da IS Ta ce Shugaban Boko Haram Shekau Ya Mutu