Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maiduguri Ta Fi Abuja Tsaro – Ali Ndume


Sanata Ali Ndume (Facebook/Muhammed Ali Ndume)
Sanata Ali Ndume (Facebook/Muhammed Ali Ndume)

"Wani zai iya zuwa ya fasa kofar gidanka da bindiga, amma a Maiduguri, ba ma ganin irin hakan.”

Sanata Ali Ndume da ke wakiltar kudancin Borno a Majalisar dattawan Najeriya ya ce ya fi samun kwanciyar hankali a Maiduguri, babban birnin jihar Borno fiye da idan yana Abuja, babban birnin kasar.

Ndume wanda shi ne shugaban kwamitin da ke kula da sha’anin dakarun Najeriya a majalisar, ya ce mafi aksarin hare-haren da mayakan Boko Haram suke kai wa a kewayen birnin na Maiduguri suke faruwa ba a ciki ba.

Ya kara da cewa, a Abuja babu irin wannan kwanciyar hankali ta fannin tsaro don a kowanne lokaci za a iya bin mutum har gida a kai masa hari.

“Ina zama a Abuja da kuma Maiduguri. Da zarar na dawo Maiduguri, na fi samun kwanciyar hankali fiye da idan ina Abuja, saboda wani zai iya zuwa ya fasa kofar gidanka da bindiga, amma a Maiduguri, ba ma ganin irin hakan.”

Ndume na magana ne a a ranar Alhamis a shirin “Politics Today” na gidan talabijin din Channels.

Kalaman nasa na zuwa ne jim kadan bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kammala wata ziyarar yini daya a birnin na Maiduguri inda ya je don duba yanayin tsaro a jihar da kuma kaddamar da wasu ayyukan da gwamnati ta kammala.

Sai dai Ndume wanda ya yi nuni da sabon kasafin kudin kasar, ya ce “al’amura za su sauya nan ba da jimawa ba.”

Ya kuma kara da cewa, sha’anin tsaro na kara inganta karkashin mulkin Buhari saboda yadda ya mayar da hankali kan inganta walwalar dakarun kasar.

Ndume ya kuma ce matsalar ta’addanci, lamarin ne da ke faruwa a ko ina a duniya ba Najeriya kadai ba.

“A Amurka, akwai matsalar harbe-harbe a makarantu, a namu bangaren, ‘yan ta’adda ne da muka sani, kuma dakarunmu suna yakar su.”

Birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya, ya kasance tunga ga mayakan Boko Haram wadanda hare-harensu suka hallaka dubban mutane suka kuma raba wasu miliyoyin da gidajensu.

Daga cikin ayyukan da Muhammaru Buhari ya kaddamar yayin ziyarar da ya kai a ranar Alhamis, har da wani rukunin gidaje da aka gina don ‘yan gudun hijira da suka rasa muhallansu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG