A Najeriya Mahara sun yi dirar mikiya a makarantar gwamnatin tarayya dake garin Birnin Yauri a jihar Kebbi inda suka dauki dalibai da kawo yanzu ba'a san adadin su ba.
Maharan a cewar wani malamin makarantar sun shiga makarantar ne suna harbin kan mai uwa da wabi inda suka firgita kowa daga nan suka fara aika- aikarsu.
Wani daga cikin iyayen da ke da yara a makarantar Malam Abdulhamid ya ce suna cikin tashin hankali.
Dan majalisar jihar Kebbi mai wakiltar karamar hukumar Ngaski ya ce da isar maharan sai da suka fara arangama da jami'an da ke tsaron makarantar kafin su samu damar shiga ciki.
Dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Yauri Shanga da Ngaski wanda yankinsa abin ya faru, ya nuna damuwa akan rashin tabuka komai tun lokacin da maharan suka shiga yankin makon da ya gabata, har suka dawo da wannan aika-aikar.
Na tuntubi rundunar 'yan sanda ta jihar Kebbi amma dai kakakin ta bai dauki wayarsa ba.
Dama jama'ar yankunan da ke fama matsalar tsaro sun jima suna kira akan a kawo masu dauki saboda halin kunci da suka tsinci kansu ciki.
Satar dalibai dai a Najeriya na ci gaba yaduwa musamman a arewacin Najeriya duk da kokarin da hukumomi ke cewa suna yi akan harkar tsaro.
Saurari Rahoto Cikin Sauti Daga Muhammadu Nasir: