Najeriya Ta Samu Karin Rana Guda Domin Kwashe Alhazan Da Suka Rage Zuwa Aikin Hajjin Bana

Wasu Alhazai masu tafiyan aikin hajji

Hukumomin Saudiya sun kara wa Najeriya kwana guda domin bada dama ga masu niyyar aikin hajji bana su iya gudanarwa, biyo bayan gaza kwashe alhazan a kan lokaci da jiragen jigila su ka yi.

Hukumomin Saudi Arabia za su rufe filin jirgin sama da ke Jeddah da karfe 12 na dare agogon Saudiyya.

A cewar Zikirullahi Hassan, a hukumance, an yi kokari an samu karin kwanaki biyu na yin jigilar alhazan kuma ya zuwa yanzu an riga an kwaso Alhazan Najeriya dubu 37 da 'yan kai domin sai da aka samo karin jiragen sama na Flynas malakin kasar Saudiyya guda biyu akan wadanda ke jigilar Alhazan tun farko wato Max Air da Azman, da Zikirullahi ya ce sun taimaka gaya wajen magance matsalar da jigilar alhazan ta fuskanta daga farkon aikin Hajjin.

Daya cikin Malaman da ke taimaka wa Hukumar wajen ilmantar da alhazan Najeriya akan yadda za su yi aikin Hajjin kamar yadda aka tanadar a adinance Ibrahim Mohammed Duguri yayi tsokaci akan aikin Hajjin na bana inda ya ce cutar da masu aikin hajji, matsallar ta na iya shafar kasar Najeriya baki daya.

Duk Alhaji ko Hajiya da aka kawo su Saudi Arabia a yau, za su hadu da 'yan'uwan su ne a Mina, domin a karfe 12 na dare agogon Saudi Arabia, kowa ya dauki harami saboda gudanar da aikin Hajjin Bana.

Saurari cikakken rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Ta Samu Karin Rana Guda Domin Kwashe Alhazan Da Suka Rage Zuwa Aikin Hajjin Bana