Shugaban kungiyar raya tattalin arziki da zamantakewa na Afirka reshen Najeriya, Ken Nnamani, ya yaba da zaben kasa da aka gudanar a Najeriya, wanda yace ya nuna irin ci gaba da kasar ta samu, musamman idan aka kwatantan zaben da aka yi a shekara ta 2007.
Nnamani, wanda shine shugaban majalisar dattijai a zamanin mulkin Obasanjo, ya bayyana haka ne a zaman bitar kungiyar domin nazari kan yadda gwamnati take karba ko akasin haka ga shawarwari da kungiyar take bata.
Ken Nnamani, wanda bai kushe gwamnatin Jonathan ba, yace jama'a suna yiwa sabuwar gwamnati ta Janar Buhari tsammani ainun. Yace, hakan ya biyo bayan irin alkawura da aka yi lokacin yakin neman zabe. Bugu da kari, babu mutumin da ya shiryawa aiki, kamar Janar Buhari, saboda ya juma yana neman wannan mukami Allah bai bashi ba sai yanzu.
Daya daga cikin wakilan kungiyoyin ayyukan tallafi masu zaman kansu da ya halarci zaman, Raymond Enoch, yace har yanzu talaka bai gani a kasa ba, musamman a banagaren ilmi da samar da kayan more rayuwa.
Sai dai Dalhatu Musa Muhammad, na kungiyar Crystal Justice, ya yi kira ga takwarorinsa cewa kada ayi riga mallam Masallaci, saboda yanzu ne ake aiki kan shawarwari da kungiyar take nufin mikawa gwamnati.
Ga rahoto
Your browser doesn’t support HTML5