Najeriya Ta Lashe Dukkan Wasanninta Na Rukuni Bayan Doke Guinea-Bissau

Your browser doesn’t support HTML5

Abin da kyaftin Troost-Ekong ya ce da Najeriya ta lashe wasanninta uku a jere bayan doke Guinea-Bissau

Dan wasan kasar Sadiq Umar ne ya fara zura kwallo a ragar Guinea-Bissau a minti na 56

Najeriya ta kara jaddada matsayinta a gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirka ta AFCON bayan da ta doke Guinea-Bissau da ci 2-0.

Wannan shi ne wasan Super Eagle na uku na kuma karshe a rukuninsu na D inda Najeriya ke jagoranci da maki 9.

Dan wasan kasar Sadiq Umar ne ya fara zura kwallo a ragar Guinea-Bissau a minti na 56 – bayan wata babbar dama da ya zubar

A minti na 75 William Troost-Ekong ya kara wata kwallon bayan wata yankar zilliya ta bajinta da Moses Simon ya yi wa masu tsaron bayan Guinea-Bissau.

An dai dauki tsawon lokacin kafin a tantance wannan kwallo a na’urar VAR mai fayyace abin da ya faru.

Da ma dai Najeriya ta riga ta kai ga zagayen ‘yan 16 tun bayan da ta lalalsa Sudan da ci 3-1 a wasanta na biyu.

A wasan na farko ta lallasa Egypt da ci daya mai ban haushi.

Wadannan nasarori suka ba ta damar darewa saman teburin rukunin na D a gasar wacce aka ake yi a Kamaru a karo na 33 yayin da Egypt ke biye da ita.

A nata bangaren, kunnen doki kawai Guinea-Bissau ta yi da Sudan, wanda ya ba ta maki daya.