Wani sabon rikici ya faru a wasan cin kofin Afirka dake gudana a Kamaru. Alkalin wasa tsakanin Tunisia da Mali ya dakatar da wasan kafin a ƙare lokacin da aka saba yi sau biyu.
Gasar ƙwallon ƙafa na cin kofin Afrika ta wannan shekarar ta sake fuskantar wani yanayi na daban a ranar Laraba, a karawar da aka yi tsakanin Tunisia da Mali .
Yayin da Mali ke kan gaba da ci daya mai ban haushi, alkalin wasan Janny Sikazwe dan kasar Zambia ya hura karshen wasan a karon farko a minti na 85.
Da ya fuskanci fushi daga na 'yan wasa da ma'aikatan Tunisia, sai ya gane kuskurensa, kuma cikin sauri ya ce a ci gaba da wasan.
A minti na 89 da dakika 45 ne ya busa karshen wasan a wannan karon, abin da ya haifar da rudani.
Kocin Tunisia Mondher Kebaier, bai boye bacin ransa ba, ya kuma yi kira da a tuntubi hukumar alkalan wasan domin gane gaskiyan lamari. Hakan bai yiwu ba. wanda jami'an tsaron filin wasan suka tilasta musu barin filin.
Daga bisani alkalan wasa sun dawo filin wasan domin ci gaba da buga sauran mintuna uku na karin lokaci a hukuncin da CAF ta yanke, amma 'yan wasan Tunisia sun ki komawa filin wasa.
A cewar wasu ‘yan jarida, ‘yan wasan Tunisia sun riga sun shiga motarsu, suna shirye da su bar filin wasan. Shi kuwa kocin na Mali, yana tsakiyar taron manema labarai ne, aka sanar da shi matakin ci gaba da wasan.