Ma’aikatar kudin Nigeria ta ceto wa gwamnatin miliyoyin nairori a bayan da ta hana ma’aikatan bogi fiye da dubu ashirin samun albashi daga aljihun gwamnati.
WASHINGTON, DC —
Jiya Lahadi ma’aikatar tace ta cire ma’ikatan bogi dubu ashirin da uku da dari takwas da arba’in da shidda daga samun albashi bayan wani bincike data gudanar, al’amarin daya samarwa gwamnati naira miliyan goma sha daya da rabi cikin wata daya.
Nigeria ta dade tana fama da matsalar cin hanci da rashawa da kuma almubazaranci.
Tun lokacinda shugaba Muhammdu Buhari ya lashi takobin yaki da cin hanci da rashawa bayan ya dare kan ragamar mulki a bara, gwamnatin sa ta dukufa wajen tsuke bakin aljihun gwamnati ko kuma rage kudaden da gwamnati take kashewa maimakon korar mutane daga aiki, domin taimakawa wajen tinkarar rikicin tattalin arziki mafi muni da Nigeria ta gani cikin shekaru da dama.