Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gallazawa Yan Gudun Hijirar Najeriya A Kamaru


'Yan gudun Hijira
'Yan gudun Hijira

‘Yan Najeriya da ke komowa daga kasar Kamaru, inda suka yi zaman hijira sun koka da abin da suka kira gallazawa da cin zarafi da hukumomin ke masu ta hanyar gallaza masu barin kasar, ba tare da kyalesu sun dauki kaddarorinsu ba alokacin da aka taso keyarsu zuwa gida Najeriya, ba tare da amincewarsu ba.

Lamarin da ya sabawa yarjejeniyar kasa-da-kasa na majalisar dinkin duniya kan al’amuran da suka shafi ‘yan gudun hijira da tsare mutuncinsu.

Wakilin sashin Hausa Sanusi Adamu wanda ya zaga sansanonin Malkohi, Fufore da Damare inda ya tautauna da wasu daga cikin ‘yan gudun hijiran sun shaida masa cewa baya ga hana su daukar mallakarsu, akwai wasu mutanen da dama da yanzu haka hukumomin Kamaru ke tsare da su a gidan kaso da ake tuhuma da aikata kananan laifuka.

Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya, Mr, Cesar Mbav Tshilombo, ya baiwa sashin Hausa tabbacin hukumar zata saurari bahasin korafe-korafe daga bakin mutane 64 daga cikin dubu 21,978 da ta maido da su gida.

Ya ce suna binciken sahihancin wadannan korafe- korafen domin gano yawan wadanda hukumomin kasar Kamaru ke tsare da su a gidajen yarinta da niyyar sake hada su da iyalansu.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG