Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mutane 40 Sun Sami ‘Yanci Daga Gidan Kurkuku A Jihar Bauchi


Gidan Yari
Gidan Yari

A jihar Bauchi wasu mutane marasa galihu guda 40 da suke tsare a gidan Kurkuku sun sami yancinsu, mutanen wanda ke tsare a gidan Yari kimanin watanni sama da Goma sun kasa biyan kudaden tara da kotu ta yanke musu.

Matar gwamnan jihar Bauchi, Barista Aisha Muhammad Abubakar, itace tayi wannan taimako na samarwa mutanen yancinsu. Bayan wata ziyara da ta kai gidan Yarin.

Wakilin Muryar Amuraka Abdulwahab Muhammad, ya tambayi Barista Aisha, dalilinta na samarwa da mutanen yanci, inda tace a baya lokacin yakin neman zabe ta samu ziyartar gidan wakafin har ta fahimci yanayin da mutanen da aka tsare suke, haka yasa tayi musu alkawarin taimaka musu ganin cewa wasu kaddara ce kawai ta kaisu.

Shugaban gidan Yarin Sidi Muhammad, yace sun ja kunnen wadanda aka sallama da cewa sake dawowa gidan kurkukun ba zai yi musu dadi ba.

Mutanen da aka samarwa yanci dai an samar musu da kayayyakin aiki, wanda kuma suke son zuwa karatu zasu sami tallafi domin zuwa karatunsu.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG