Jakadan kasar Canada a Najeriya, Perry John Calderwood, yace yaduwar cututtuka a kasa da ketare ka iya gagarumin tasiri wajen gurgunta tattalin arzikin kasa. Ya ci gaba da cewa karfafa tsaron lafiya batu ne muhimmi da ke bukatar yunkurin kasashen duniya ta bangarori daban daban.
Calderwood yace gwamnatin kasar Canada, zata ci gaba da karfafa dadadden dankon zumunci da ke tsakaninta da Najeriya, ta hanyar inganta dakin binciken. Jakadan yace dakin binciken zai iya gano cututtuka kamar su zazzabin shawara da hawkan kare da cutar murar tsintsaye da kuma zazzabin Lasa da dai sauran cututtukan dake yaduwa cikin hanzari.
Ministan Noma da raya karkara Audu Ogbeh, yace a farkon wannan shekara Najeriya tayi asarar Kaji tsakanin Miliyan 300 da Miliyan 500 saboda bullar cutar murar tsintsaye.
Domin karin bayani.