Najeriya Na Sa Ran Samun $1.5m Daga Tsarin Tattalin Arzikin Halal

Kashim Shettima (Facebook/Bola Ahmed Tinubu Support Group Germany)

A bisa kididdigar da ake da ita, tsarin tattalin arzikin halal na duniya na da jarin daya kai dala tiriliyan 7 kuma ana hasashen cewar zai bunkasa da dala 7.7 kan nan da 2025.

Mataimakin Shugaban Najeriya Kashin Shettima yace kasar ta rungumi tsarin tattalin arzikin halal kuma ta na fatan yin amfani da damar wajen kara kudin shigarta da dala 1.5m kan nan da 2027.

Shettima ya bayyana hakan ne yayin daya halarci taron masu ruwa da tsaki a Abuja a yau Laraba.

A halin yanzu akwai fiye da kayayyakin kasuwanci 100 da aka tantance a matsayin halal a Najeriya.

A bisa kididdigar da ake da ita, tsarin tattalin arzikin halal na duniya na da jarin daya kai dala tiriliyan 7 kuma ana hasashen cewar zai bunkasa da dala 7.7 kan nan da 2025.

Kashin Shettima ya kara da cewar gwamnatin najeriya zata ci gajiyar damammakin da kasuwar halal din zata samar.