Gwamnatin Tarayya na dab da fara aiwatar da shirinta na tillastawa hukumomi da ma’aikatun gwamnati ware kaso 5 cikin 100 na guraben aikin yi ga masu bukata ta musamman a fadin Najeriya.
Babban Hadimin Shugaban Kasa Bola Tinubu akan Masu Bukata Ta Musamman, Muhammad Abba-Isa ne ya bayyana hakan a birnin Damaturu, fadar gwamnatin jihar Yobe, a yayin wata ganawa da masu bukata ta musamman da sauran masu ruwa da tsaki bayan bashi mukamin.
Ya bayyana cewar offishinsa na aiki kafada da kafada da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya domin tallafawa masu buakata ta musamman, da nufin rage su akan tituna suna barace-barace.
“Wajibi ne hukumomi da ma’aikatun gwamnati su warewa masu bukata ta musamman kaso 5 cikin 100 na guraben aikin yi, domin hanya daya tilo ta rage musu radadin rayuwa ita ce ta samu musu ayyukan yi da tallafi.
“Kuma ita ce kadai hanyar magance yawan barace-barace kuma nan gaba kadan Shugaban Kasa zai bayyana shirye-shirye da tsare-tsare akan hakan”.
“An riga an fitar da sanarwa daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya da nawa ofishin domin yin matsin lamba ga hukumomin. Muna da shiri a kasa, abinda ke mana cikas kawai shine, yadda za’a aiwatar da shirin.” a cewar Abba Isa.