Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Sarakuna Da Ake Zargi Da Tsoma Baki A Al'amuran Siyasa Na Dakon Hukunci A Sakkwato


Fadan Mai Alfarma, Sarkin Musulmi, Muhammadu Saad Abubakar, a Sakkwato, Arewa Maso Yammacin Najeriya.
Fadan Mai Alfarma, Sarkin Musulmi, Muhammadu Saad Abubakar, a Sakkwato, Arewa Maso Yammacin Najeriya.

Wasu sarakuna da suka hada da 'yan majalisar Sarkin musulmi na dakon fuskantar hukunci, sakamakon wani kwamiti da gwamnatin Sakkwato ta kafa don gudanar da bincike akan zarginsu da aikata laifuka masu alaka da siyasa.

Ana daukan sarakuna a matsayin iyayen al'umma, bisa la'akari da gagarumar gudumawar da suke bayarwa wajen daidaita al'amurra a cikin al'umma da kuma ci gaban al'ummar yankunansu.

To, sai dai a wasu lokutan kuma, sarakunan sukan fada tsaka mai wuya musamman ma idan an tuhume su da tsoma baki a lamuran siyasa ko kuma wasu lamura masu alaka da siyasar, abin da kan kai ga cire sarki ko a rage masa daraja, kamar yadda ya sha faruwa a wasu jihohin a Najeriya.

A yanzu haka a jihar Sakkwato akwai sarakunan da ke dakon hukunci biyo bayan gurfanar da su da gwamnatin jihar ta yi gaban wani kwamiti akan tuhumar sun taka rawa ga jam'iyyar adawa ta PDP a lokacin zabubuka da suka gabata.

Wakilin Muryar Amurka a Sakwato Muhammad Nasir, ya nemi jin ta bakin wasu daga cikin sarakunan da lamarin ya shafa amma sun ki cewa uffan.

Sai dai wata majiya kwakkwara na kusa da wasu daga cikin sarakunan, tace lallai an baiwa sarakunan goron gayyata a ranar Laraba na makon da ya gabata inda aka ce su bayyana gaban kwamitin a ranar Alhamis kuma cikinsu akwai 'yan Majalisar Mai Martaba, Sarkin Musulmi, biyar da wasu uwayen kasa, inda aka karanta musu korafe-korafen da aka ce wasu mutanensu sun yi akan su.

Duba da cewa an tuhumi sarakunan akan goyon bayan jam'iyar PDP, wakilin Muryar Amurka ya nemi jin ta bakin jam'iyyar ta PDP akan wannan batu.

On the left is the Emir of Mafara, Alhaji Bello Mohammadu Barno, who representated the Sultan of Sokoto.
On the left is the Emir of Mafara, Alhaji Bello Mohammadu Barno, who representated the Sultan of Sokoto.

Sakataren Yada Labaru na jam'iyyar PDP Hassan Sahabi Sanyinna yace a ra'ayinsu, sarakuna iyayen al'umma ne ba 'yan siyasa ba, amma kuma ba za su yi mamaki ba idan gwamnatin Sakkwato ta shirya cin zarafin sarakuna domin gwamnatin wadda 'yan APC na yanzu suka yi, ta saba yin hakan.

Shi kuma Kakakin Jam'iyyar APC, mai mulkin Sakkwato Sambo Bello Danchadi, yace gwamanatinsu mai adalci ce kuma zata yi adalci ga kowa, ya kuma ce korafin da jam'iyar PDP ta yi zargi ce kawai.

Da wakilin Muryar Amurka, Muhammad Nasir ya tuntubi jami'in hulda da jama'a a fadar Sarkin Musulmi akan wannan batu, yace ba su da masaniya a kan wannan lamarin.

Tun kafin wannan lokaci dai, jama'a na ganin akwai tsamin dangantaka tsakanin gwamanati mai mulki yanzu da fadar mai alfarma, Sarkin Musulmi, abinda watakila baya rasa nasaba da kalaman da Mataimakin Shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shatima, ya yi a wani lokaci da ya kai ziyara Sakkwato.

Yanzu dai sarakunan da ma sauran jama'a sun zura idanu su ga yadda sakamakon da kwamitin zai bayar, da kuma matakin da gwamnatin jihar zata dauka.

A saurari rahoton Muhammad Nasir:

Anyi Zargin Wasu Sarakuna Da Tsoma Baki A Lamuran Siyasa A Sakkwato.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG