Wata sanarwa da Kakakin shugaban Najeriyar, Ajuri Ngelale ya fitar ne ya sanar da matakin dakatar da ministar a yau.
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne domin ba da dama ga hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gudanar da bincike a kanta.
Shugaba Tinubu ya jaddada bukatar gudanar da cikakken bincike don tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen amfani da kudaden jama’a da aka ware domin ayyukan jin kai da kuma kawar da fatara.
An umurci ministar da aka dakatar, Dr. Betta Edu da ta mika aikinta ga babban sakatariyar ma’aikatar jin kai da yaki da fatara ta tarayya.
Bugu da kari, shugaba Tinubu ya bukaci Dakta Edu da ta baiwa hukumomin bincike cikakken hadin kai a yayin binciken.
Ana zargin Ministar da bada umurnin tura kudi kimanin naira miliyan 585 zuwa asusun banki na wata mata daban.
Hakan na zuwa ne jim kadan bayan wasu kungiyoyi masu zaman kansu su ka bukaci gwamnatin Shugaba Tinubu ya yi cikakken bincike a Ma'aikatar .
Tun farko farkon dambarwar kan zargin da ake yiwa ministar al’ummar Najeriya da dama musamman a kafafen sada zumunta sunyi ta kiraye-kiraye kan a dakatar da Ministar don baiwa hukumomi damar bincike game da zarge zarge da ake yi mata.
Ana sa ran wannan matakin zai maido da kwarin gwiwa kan kudirin gwamnatin na kawar da cin hanci da rashawa a cikin cibiyoyin gwamnati.
Al’ummar kasar dai na jiran sakamakon binciken hukumar EFCC da kuma sakamakon binciken kwamitin da ke neman sauyi a daidai lokacin da jama’a ke ganin shugaba Tinubu ke daukar kwararran matakai na tabbatar da kyakkyawan shugabanci da kuma amfani da dukiyar al’umma yadda ya kamata domin ci gaban al’ummar Najeriya.
Dandalin Mu Tattauna