Wannan Hukuma dai an kafa ta ne tun shekaru 11 da suka wuce domin ta taimaka wajen karfafa wa da sake farfado da tsarin karbo kudade ta yadda za a magance matsalolin kadarorin rance da ake karba a bankuna yadda ya dace.
Sai dai Babban Darekta a Hukumar AMCON Ahmed Lawal Kuru ya ce akwai kalubale da yake fuskanta, saboda a cewar shi, duk wadanda suka karbi wadannan kudade, manyan mutane da kanana, wadanda suke gudu a duk lokacin da aka neme su.
Ahmed Kuru ya ce ba sa yarda su bada takardun kaddarori da suka mika a matsayin lamuni waje karban bashin, saboda haka AMCON ta kawo kuka zuwa majalisa domin neman taimako.
Karin bayani akan: naira, AMCON, Majalisar Dattawan Najeriya, Nigeria, da Najeriya.
Amma daya cikin 'ya'yan kwamitin kula da Bankuna da Kamfanonin Inshora Sanata Mohammed Adamu Aliero, ya ce Majalisa za ta tabbatar da cewa an kar6o wadanan kudaden saboda suna da yawa kuma a hanun mutane 20 kachal
Adamu Aliero ya ce Najeriya tana cikin halin ha'u'la'i a fannin tattalin arzikin ta, akan haka ne Majalisa ta amince da dokar.
Shi kuwa Shugaban Komitin Kula da Bankuna da Kamfanoni Inshora Sanata Uba Sani ya ce an kafa AMCON shekaru 11 kenan da suka wuce amma dokar da ta kafa hukumar bata ba hukumar karfi na kar6o kudade da kaddarorin Gwamnati kamar yadda ya dace ba, shi ya sa ya kawo dokar da za ta yi kwaskwarima akan dokar da ta kafa hukumar.
Uba Sani ya ce a sabuwar dokar za a kafa Kotu na musamman ko TRIBUNAL a turanci wacce za ta iya kar6o kudaden a hannun wadanda suka ci bashin su, a wani bangare kuma ana iya hukunta wanda bai biya ba.
A lokacin da ya ke nazari akan batun, kwararre a fannin tattalin arziki Kassim Kurfi ya ce wanan mataki yana da kyau, domin in an samu wadanan kudade, za a iya farfado da masana'antu da zai bada dama matasa su samu aiyukan yi.
Abin jira a gani shi ne yadda wanan kotu da za a kafa zai taimaka wajen kwato wadanan makudan kudade da dukiyoyin Gwamnati don sanya su a fa'idar tattalin arziki ba tare da wata matsala ba.
Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5