Najeriya: Kungiyar Kwadago Za Ta Yi Zanga-zanga Ranar Alhamis

NLC (file photo)

Kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta baiyana aniyar gudanar da zanga-zangar nuna damuwa ga abun da ta kira rashin tsayin daka kan yaki da cin hanci da kuma tsadar rayuwa.

Kungiyar karkashin Kwamrad Ayuba Wabba, ta shirya gudanar da zanga-zangar ranar alhamis din nan 9 ga watan nan na Fabarairu a Abuja.

Jami’in kungiyar Kwamrad Nuhu Toro, ya ce kungiyar za ta ziyarci ofishin hukumar yaki da cin hanci da kuma majalisar dokokin Najeriya inda za ta mika wasikun korafin na su.

Kungiyar za ta yi amfani da damar wajen kokawa ga bukatar kara mafi karancin albashi daga Naira dubu 18,000 zuwa 58,000.

Toro ya ce zanga-zangar ta su ba ta da nasaba da wacce wassu kungiyoyin siyasa da farar hula su ka yi a farkon mako.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Kungiyar Kwadago Za Ta Yi Zanga-zanga Ranar Alhamis - 2'57"