Albarkacin ranar yaki da dabi’ar yiwa mata kaciya da ake shagulgulan karramawa a ko ina a fadin Duniya, kungiyoyin dake wannan yaki a jamhuriyar Nijar sun bayyana yiyuwar kawo karshen wannan mummunar dabi’a kafin wa’adin kawo karshenta da Majalisar Dinkin Duniya ta ‘dauka na shekarar 2030.
Duk da yake hukumomi na yin iya bakin kokarin a yaki da yiwa mata kaciya a jamhuriyar Nijar, kungiyoyin masu zaman kansu basu yi ‘kasa a gwiwa ba wajen wannan fafutuka domin murkushe ‘dabi’ar a ‘kasar da MDD ta gano cewa kashi biyu daga cikin ‘dari na ‘yan mata ne ke fuskantar wannan matsala, alamar samun ci gaba a yakin.
Hajiya Maimuna ta kungiyar CONIPRAT tace ya samo asali daga ayyukan wayar da kan al’umma, kasancewar yadda kaciyar kan harfar da illa ga ‘ya ‘yan matan da aka yiwa, wanda wasu lokutan ma kan zama ajali.
Yankunan TiIlaberi da Yamai da wani bangare na jihar Diffa sune su kayi fice wajen yiwa ‘yan mata kaciya a Nijar, wanda yasa hukumomi a shekarar 2003 kafa dokar haramta al’adar a fadin kasar baki ‘daya.
Sai dai bayanai na nuna yadda sako-sakon da aka yi wajen zartar da wannan doka ya rage armashin yakin da aka sa gaba, inji Hajiya Fatima jagora a wannan tafiya, wadda tace suna nan suna yin kokarin ganin an tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da laifin sabawa dokar.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Mumuni Barma.