Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Zanga-zangar Nuna Adawa Da Tsadar Rayuwa


Masu zanga-zanga
Masu zanga-zanga

Daruruwan ‘yan Najeriya ne suka gudanar da zanga zangar lumana a wasu titunan Lagos da Abuja domin nuna adawa da tsadar rayuwa a Najeriya.

Da farko dai sanannen mawakin nan mai suna Tupace, shine ya shirya gangamin kafin daga baya ya bada sanarwar janyewa, sai dai wasu kungiyoyi sun jagoranci zanga-zangar a biranen Legas da Abuja. Duk da yake ‘yan sanda sun hana masu zanga-zangar halartar wani maci a dandalin Unity dake Legas.

Masu zanga-zangar dai sun fito ne domin nuna rashin amicewarsu ga tsadar rayuwa da suka alakanta da manufofin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, da yanzu haka yake hutu da jinya a London.

Daruruwan masu zanga-zangar dai sun fito ne dauke da kwalaye da rubutu a jikinsu, wadanda ke nuna fushinsu ga halin da talakan Najeriya ya tsinci kansa.

Rahotanni na cewa an gudanar da ire-iren wannan zanga-zanga a wasu manyan birane na kasar da suka hada da birnin Legas da Abuja da Fatakwal na jihar Rivers.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG