Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce Rundunar Kai Farmaki ta Thunder Strike ta yi ta barin wuta akan wasu sansanonin yan bindiga biyu a jihar kaduna.
Hare Haren da jiragen yakin kasar suka kaddamar a dazukan Kuduru da Kwiambana a jihar ta Kaduna sun yi sanadin kashe ‘yan ta'adda da dama a dazukan.
Kwamandan Dakarun Ruwa (Navy Commander) Abdulsalam Sani na Hedikwatar tsaron kasar ya shaida wa muryar Amurka cewa jiragen yakin, kazalika sun rugurguza sansanonin ‘yan ta'addan.
Hedikwatar tsaron Najeriyar ta ce hare haren za a ci gaba da kai wa ne har sai an kawo karshen aika aikar ‘yan bindigar a sassan jihar.
Kwamanda sani ya kara da cewa wannan na zuwa ne bayanda a makon jiya su ma sojojin kasa sukai wa wasu masu garkuwa da mutane kwanton bauna, inda suka halaka hudu daga cikinsu.
A bangarenta, gwambatin jihar kaduna, ta bakin kwamishinan harkokin tsaro na jihar, Samuel Aruwan ta yaba da wannan ci gaba, inda shima ya tabbatar da za a ci gaba da kai hare haren.
Aruwan ya ja hankalin jama’ar jihar cewa kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta bai da alaka da addini ko kabilanci, inda yace aika aika ne kurum na ‘yan ta'adda, kuma gwamnati na aiki tukuru don yi wa tubkar hanci.
Inda ya bayyana kwarin gwiwar maido da cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar nan bada jimawa ba.
Ga wakilin Sashen Hausa Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5