Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Addinai Sun Nemi Hanyar Shawo Kan Rikici a Jihar Kaduna


KADUNA: Rikicin Kafanchan
KADUNA: Rikicin Kafanchan

Kungiyoyin addini a jihar Kaduna sun fito da hanyoyin warware abubuwan da ke sabbaba hare-hare a yankin sakamakon ci gaba da tashin hankali da ake fama da shi a kudancin kasar.

Majalissar koli ta tabbatar da shari'a reshen Kaduna ta ce mafita kawai ita ce hukunta masu laifi da kuma taron sulhu tsakanin al-umar yankin.

Majalissar da ta kira taron manema labaru don nuna damuwa game da rashin zaman lafiya a kudancin Kaduna ta ce matukar gwamnati ba za ta hukunta masu laifi ba, to rikici ba zai kare ba.

A cikin hirar sa da Sashen Hausa, Malam Abdurrahman Hassan, sakataren majalisar ta kolin ya bayyana cewa, gwamnati ta kakkafa kwamitoci a lukutan baya da nufin neman hanyar shawo kan matsalar sai dai rashin aiwatar da shawarwarin kwamitin ne sanadin ci gaba da tashin hankali domin ba a hukunta wadansu ba ya zama ishara ga masu neman tada fitina.

A nata bangaren, kungiyar Kiristoci ta Najeriya wato CAN tana da ra'ayin cewa matsala ce ta cikin gida dake bukatar al-umar yankin su zauna su tattauna. shugaban kungiyar CAN a jahohi sha tara na Arewacin Najeriya Reverend Yakubu Pam ya ce an jima ana fama da rikicin sabili da haka al’ummar yankin ya kamata su zauna su tattauna, su fahimci juna.

A da dai hare-haren 'yan-bindiga sun addabi al-umar yankunan Kerawa, Giwa, Birnin Gwari kawai a jahar Kaduna kafin daga bisani kuma suka koma yankin kudancin Kaduna inda aka hallaka mutane da kuma jikkata wasu da dama.

Saurari cikakken rahoton Isa Lawal Ikara cikin sauti,

Kungiyoyin Addinai Sun Nemi Hanyar Shawo Kan Rikici a Jihar Kaduna:3:20"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG