Sai dai masana harkokin doka na ganin lokaci yayi da manyan alkalan kasar za su rinka amfani da damar da suke da ita wajen yanke hukuncin shari’u akan lokaci domin kauce yanayin take hakkin dan Adam.
Batun take hakkin bil’adama na ci gaba da zama ruwan dare a Najeriya a matakai daban-daban, duk kuwa da karuwar alkaluman kungiyoyin kare hakkin dan Adam da ake samu a kasar.
Sai dai kungiyoyin na kokawa kan irin kalubalen da suke fuskanta wajen bibiyar hakkin masu rauni. Alhaji Bello Gadon Kaya, shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam ta human rights foundation of Nigeria. Ya yi kira ga alkalai da cewa su rika saka ido da tabbatar da an kammala duk shari’ar da aka gabatar garesu ba tare da bata lokaci ba.
Batun ‘yancin bil’adama na cikin al’amuran da suka mamaye ajandar taron kungiyar lauyoyi musulmi ta Najeriya daya gudana a jihar Kano.
Barrister Ibrahim Yakubu Umar tsohon kwamishinan shari’a na jihar Bauchi ne ya ce taron ya zaburar da manyan alkalai ta wannan fuska.
Tuni dai kungiyoyin ketare irin su Amnesty International suka rinka wallafa rahotanni kan zargin jami’an tsaron Najeriya da take hakkin bil’adama.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5