Najeriya Da Nijar Zasu Mayar Da Hankali Wajen Inganta Tafkin Chadi

Shugaba Buhari Da Takwaransa Na Kasar Nijar

A ci gaba da tattaunawar da akeyi game da muradun ‘karni a zauren taron Majalisar Dinkin Duniya, shugabannin nahiyar Afirka wanda suka hada da Najeriya da Nijar sun mayar da hankali akan yadda zasu inganta tafkin Chadi.

Cikin bayaninsa shugaba Mohammadu Buhari yace gwamnatin tarayyar Najeriya zata yi duk abin da yakamata ta yi domin ganin an inganta yankin tafkin Chadi. Kuma zata ci gaba da hada kai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar Muhalli, musamman kan batun tafkin Chadi da sauran al’amura da suka shafi muhalli.

Buhari yace yadda gwamnatinsa ta tunkari share yankin Ogoni ba da wasaba haka zata mayar da hankali domin ganin ta cimma burinta game da yankin tafkin Chadi. Dukkanin shugabannin biyu sunyi amince da cewa a kwai bukatar su tashi tsaye game da yankin, domin kuwa bayan kyautata Muhalli zai kuma samar da aikin yi ga dinbin jama’a.

Sai dai shugabannin na ganin akwai bukatar kasashe masu karfin tattalin arziki su matso kusa domin bayar da gudunmawarsu, muddin da gaske suke na cewa suna son Duniya ta zauna lafiya.

Saurari cikakken rahotan Ladan Ibrahim Ayawa.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Da Nijar Zasu Mayar Da Hankali Wajen Inganta Tafkin Chadi - 3'35"