Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farashin Shinkafa Ya Fadi A Jihar Gombe


Yan Kasuwa Na Auna Shinkafa
Yan Kasuwa Na Auna Shinkafa

Bincike ya nuna cewar sanadiyar shigowar sabuwar Shinkafar da aka shuka a damunar bana kasuwa, ya kawo saukin kudin Shinkafar.

Abdulhamid Mohammad wanda aka fi sani da suna Danladi Tula, shine shugaban masu fataucin Shinkafa a jihar Gombe, ya tabbatar da faduwar farashin shinkafa ya fadi ‘kasa yana mai cewa ikon Allah ne ya kawo wannan sauki, domin lokacin da ta tashi basu bane suka ‘kara kasuwace.

Shinkafa da ake kira da suna Jamila wadda itace tafi kowacce kyau, yanzu haka a Gombe ana sayar da ita N25,000 sakamakon ‘yan kwanakin da suka gabata an sayar da ita N37,000. Akwai kuma wata karama da ake sayarwa akan kudi N30,000 yanzu kuma ta dawo N18,000.

Yanzu dai ‘yan kasa zasu fara sa rai ga yiwuwar sauran al’amura zasu dai dai ta, ganin cewar kudin cimaka ya fara yin kasa.

Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Mohammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG